Babban sufeton yan sandan Nijeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, Ph.D. NPM, ya jagoranci kaddamar da wasu sabbin gine-gine da suka hada da dakunan kwana da ofisoshi, wadanda aka gina a barikin yan sanda na Bompai da kuma Zariya Road.
Wannan nada daga cikin shirin babban sufeton yan sandan na kara inganta walwalar dakarun rundunar tare da kara musu kwarin gwiwa wajen yin aiki tukuru.Shugaban yan sandan ya fara da ziyartar shelkwatar
rundunar, inda aka yi masa faretin girmamawa tare da
gaisawa da manyan jami’an ‘yan sandan jihar kafin ya
wuce wurin da aka gudanar da taron.
Kayode ya kaddamar da sabbin dakunan kwana na zamani sama da 300, ofisoshi 48, wurin gyaran mota, wuararen ibada da kuma samar da hanyoyi a cikin barikin dake Bompai.
Kwamishinan yan sandan jihar Kano CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa tun lokacin da yakama aiki a jihar, rundunar ta samu nasarori wajen yaki da masu aikata, tare da tabbatarwa da alumma cewa za su ci gaba da wanzar da zaman lafiya da kuma kare rayukansu da dukiyoyinsu.
- Kwamishinan Da Ake Zargi Da Belin Mai Safarar Kwayoyi Ya Yi Murabus
- Babban Sufeton Yan Sandan Nijeriya Kayode Egbetokun Zai Ziyarci Jihar Kano

CP Bakori ya godewa babban sufeton yan sandan bisa kaddamar da wannan muhimmin aiki don kara inganta walwalar yan sandan.
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda ya samu wakilcin kwamishinan tsaron cikin gida , AVM Ibrahim Umar mai ritaya, a madadin gwamnati da kuma al’ummar jihar ya mika godiyarsa ga sufeton yan sandan bisa kawo wannan ci gaba don kara inganta walwalar yan sandan jihar.
Babban sueton yan sandan IGP Kayode Adeolu , ya nuna matukar godiyarsa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, bisa goyon bayan da yake ba wa rundunar ‘yan sandan Nijeriya , wanda a cewarsa shi ne ya amince da yin wannan gyare-gyare.

