Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), a Jihar Kebbi, ta bayar da takardar shaidar lashe zabe ga zababben gwamnan jihar, Nasir Idris da mataimakinsa Umar Abubakar da ‘yan majalisar dokokin jihar 10.
Farfesa Muhammad Sani Kalla, Kwamishinan INEC na kasa mai kula da jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara, ya kuma bayar da takardar shaidar cin zabe ga wasu zababbun ‘yan majalisar dokokin jihar a zaben da aka kammala.
Jihar na da mazabu 24, sannan kuma INEC a ranar 30 ga watan Maris ta gabatar da takardar shaidar cin zabe ga mutane 14 da suka yi nasara a zaben majalisar dokokin jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Jim kadan bayan karbar shedarsa ta cin zaɓe Dokta Nasir Idris, zababben gwamnan jihar ta Kebbi, ya yaba wa hukumar, da hukumomin tsaro bisa yadda jama’a suka gudanar da zabe ba tare da wata matsala ba a cikin fadin jihar baki daya.
Ya kuma mika godiyarsa ga wadanda suka zabe su bisa yadda suka tabbatar da an gudanar da aikin cikin nasara, ba tare da wata matsala ba, ya kuma roki Allah da ya ba su ikon yi wa al’ummarsu adalci a yayin tafiyar da mulki a jihar.