Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP, ya bayyana cewa takarar da ya yi da wasu mutane ne masu karfin fada-a-ji da ke Abuja, ba da Aishatu Binani ba.
A jiya Talata ne hukumar zabe ta INEC ta ayyana Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben jihar ta Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Fintiri ya ƙara da cewa ba da wata mata (Binani) ya yi takara ba, ko jam’iyyar APC, ya yi takara ne da wasu masu madafun iko da ke Abuja, wadanda suke tunanin su suka mallaki Najeriya
Sai dai gwamnan na Adamawa bai kama sunan wadanda yake ikirarin da su ya yi takara ba.
Fintiri ya samu kuri’u 430, 861 a zaben da aka sake a jihar a ranar Asabar din da ta gabata yayin da Aishatu Binani ta APC ta samu kuri’u 396, 788.
An yi ta kai ruwa rana yayin tattara sakamakon zaben, lamarin da ya haifar da rudani a lokacin da aka ayyana Binani a matsayin wacce ta lashe zabe, ko da yake hukumar INEC ta soke wannan matsaya.
A ranar 29 ga watan Mayu za a sake rantsar da Fintiri a wa’adin mulki na biyu.