Hukumar zaben mai zaman kanta ta yi iƙirarin daukar matakin shari’a kan jam’iyyar PDP da wasu masu yada jita-jta da ba su da tushe bale makama akanta ga shugaban hukumar farfesa Mahmood Yakubu.
Baban jami’in yadda labarai na hukumar Rotimi Lawrence oyekanmi ne ya yi wannan gargadin a yammacin jiya a babban birnin Tarayya Abuja.
A safiyar jiya ne juma’a, ne jam’iyyar PDP ta yi taron manema labarai, inda ta zargi shugaban hukumar zabe farfesa yakubu da yin magudi a zaben shugaban kasa da na yan majalisun jahohi da ya gabata a ranar 25 ga watan fabrairun shekarar 2023 sannan sun ƙara dacewa hukumar zaben na shirin yin magudi a zaben gwamnoni da na yan majalisun tarraya da za ayi a ranar 18 ga watan maris din shekarar da muke ciki da kuma rashin ƙin amfani da nau’urorin Bvas.
Duk da haka oyekankanmi ya bayyana cewa kiran da PDP ta sake yi wa shuguban hukumar zabe farfesa mahmood yakubu kan yin murabus daga kujerarsa na shugabanci kuskure ne.