• Home  
  • Injin Casar Shinkafa Ya Halaka Wata Mata A Gombe
- Babban Labari - Labarai

Injin Casar Shinkafa Ya Halaka Wata Mata A Gombe

Wata matar aure mai suna Hauwaʼu Abubakar, ’yar shekara 32, ta riga mu gidan gaskiya bayan da injin casar shinkafa ya ja rigarta a Tumu, cikin Ƙaramar Hukumar Akko ta Jihar Gombe.

Wata matar aure mai suna Hauwaʼu Abubakar, ’yar shekara 32, ta riga mu gidan gaskiya bayan da injin casar shinkafa ya ja rigarta a Tumu, cikin Ƙaramar Hukumar Akko ta Jihar Gombe.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 8 ga Satumba, 2025.

Ya ce, Hauwaʼu ta je wajen wani mai injin casar shinkafa, Muhammad Danjuma, mai shekara 29, domin sayen shinkafa. Sai dai yayin da injin ke aiki, tufafinta ya makale a bel ɗin injin, ya janyo wuyar ta har samu mummunan rauni a wuyanta.

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Gombe, Bello Yahaya, ya yi ta’aziyya ga iyalan mamaciyar da mazauna yankin, yana mai bayyana wannan rashi a matsayin abin bakin ciki.

Rundunar ’yan sandan ta kuma gargadi jama’a musamman masu amfani da injina su kula da tsaron lafiyarsu ta hanyar:

  • Gujewa kusantar inji yayin da yake aiki.

  • Sanya kayan kariya a wuraren injiniya.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai