Rundunar yan sandan Nijeriya ta tabbatar da cewa, jami’an tsaron kasa da kasa na Interpol, sun dawo da matashin nan mai suna, Benjamin Best Nnayereugo, wanda akafi sani da Kilaboi daga kasar Qatar bisa zarginsa da halaka wata budurwarsa bayan sun samu sabani a gidansa dake jihar Legos.
Kakakin rundunar yan sandan Nijeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi,, ta cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar , ya ce wanda ake zargin ne ya kashe Oseodion Onuwabhagbe mai shekaru 21 a duniya, wadda daliba ce a jami’ar Lead City dake Ibadan, kuma an dawo dashi ne don ya fuskanci hukunci.
Rahotanni na cewa Benjamin ya halaka dalibar a ranar 13 ga watan Yuli 2023 a gidasa dake jihar Legos, inda ya tsere zuwa kasar Saliyo (Sierra Leone) don gujewa hukuma.
Sai dai a kasar Saliyon an kama shi tare da tsare shi a gidan yari, kafin ya samu damar tserewa daga gidan yarin zuwa kasar Qatar, inda yake amfani da sunan bogi na, Taure Abdoulaye, a jikin Fasfo dinsa a kasar Qatar.
- NDLEA TA Gina Gidan Gyaran Tarbiyyar ‘Yan Shaye-shaye A Kano
- Masu Garkuwa Sun Nemi Kudin Fansa 300m Kafin Su Saki Dan Kasar Chaina Da Suka Sace A Abuja
Sanarwar ta kara da cewa Benjamintun bayan da ya aikata laifin ya yi yawo a kasashe da dama ciki harda afrika ta tsakiya da gabashin asiya da gabas ta tsakiya tare da yin amfani da sunayen karya kafin ya dawo kasar Qatar a ranar 24 ga watan Janairu 2025.
An kama shi ta hanyar hadin gwiwar jami’an tsaron kasa da kasa da kuma amfani da na’urorin zamani don gano mutanen da ake nema a ofishin Interpol na Abuja da kuma ofishin Interpol na Doha babban birnin kasar Qatar, wanda ya kai ga kamashi a watan Fabarairu 2025.
bayan kama shi ne aka turo da bukatar dawo dashi Nijeriya, ta hannun ma’aikatar shari’a dake Abuja, wanda kotun kasar Qatar ta amince da hakan sannan aka dawo dashi a ranar Asabar.