• Home  
  • Masu Garkuwa Sun Nemi Kudin Fansa 300m Kafin Su Saki Dan Kasar Chaina Da Suka Sace A Abuja
- Babban Labari - Labarai

Masu Garkuwa Sun Nemi Kudin Fansa 300m Kafin Su Saki Dan Kasar Chaina Da Suka Sace A Abuja

Wasu yan bindiga da ba a san ko suwaye ba, sun sace wani dan kasar chaina mai suna Yangi Ming, a birnin tarayya Abuja, inda suka nemi kudin fansar naira miliyan 300. Rahotanni na cewa ,Yangi, yana aiki ne babban kantin Panda Supermarket, kuma an sace shi da misalin karfe 5pm sanye da gajeren wando […]

Wasu yan bindiga da ba a san ko suwaye ba, sun sace wani dan kasar chaina mai suna Yangi Ming, a birnin tarayya Abuja, inda suka nemi kudin fansar naira miliyan 300.

Rahotanni na cewa ,Yangi, yana aiki ne babban kantin Panda Supermarket, kuma an sace shi da misalin karfe 5pm sanye da gajeren wando mai launin ruwan kasa da bakar riga a yankin Durimi Abuja.

Wata yar uwarsa mai suna, A’isha Pan, mazauniyar Sharada Kano, ita ce ta samu kiran masu garkuwar da mutanen inda suka bukaci a biyasu naira miliyan 300 kafin su sake shi.

Kawo yanzu dai rundunar yan sandan birnin tarayya abuja , bata ce komai ba kan wannan lamari.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai