Hukumar Gudanarwar Masallatan Harami dake ƙasar Saudiyya ta tabbatar da ritayar Sheikh Sa’ud Ibrahim Shuraim, daga yin limanci a Masallacin Harami da ke Makkah.
Hukumar ta kuma sanar da haka ne daren jiya, Alhamis, a sanarwar da ke dauke da jerin jadawali da jerin sunayen limaman da za su jagoranci sallolin Tarawih da Tahajjud a masallatan Harami a watan Ramadan na shekarar 1444 Hijiriyya da zai kama a mako mai zuwa.
Sanawar ta bayyana cewa bayan amincewar Masarautar Saudiyya da ritayar Sheikh Sa’ud Shuraim ba zai jagoranci sallolin Tarawih da Tahajjudi a bana, a Masallacin Haramin Makkah da ya saba limanci ba. Wadanda za su yi limancin sallolin su ne:
1. Sheikh Abdul Rahman Sudais
2. Sheikh Bandar Baleelah
3. Sheikh Maher Al Muaiqly
4. Sheikh Yasir Ad Dawsary
5. Sheikh Abdullah Juhany
Sheikh Shuraim ya yi ritaya daga matsayinsa na daya daga manyan limaman masallacin ne bayan shekara 32 yana gabatar da hudubobi da jagorantar Sallar Juma’a da sauran salloli.
A ranar 6 ga watan Oktoba, 1991 ne aka nada Sheikh Shuraim limamin Masallacin Harami saboda dalilai na kashin kansa.