Home » Dalilan Sauya Kwamishinonin ‘Yan Sanda Sau 5 a Kano

Dalilan Sauya Kwamishinonin ‘Yan Sanda Sau 5 a Kano

by Anas Dansalma
0 comment

Bincike ya nuna cewa sau biyar Rundunar ’Yan Sanda ta ƙasa ta nada tare da sauya kwamishinan ’Yan Sanda da ta turo nan Jihar Kano.

Wannan dambarwa na da nasaba da Siyasar Kano gabanin zaben gwamnoni da ’yan majalisar dokokin jiha da za a gudanar ranar Asabar, 18 ga watan Maris ɗin da muke ciki.

Idan za a iya tunawa a baya, Jam’iyyar APC mai mulkin jihar da kuma manyan jam’iyyun adawarta a jihar, irin su NNPP da PDP sun zargi wasu daga cikin Kwamishinonin ’Yan Sandan da aka sauya da shiga harkokin siyasar jihar.

Idan za a iya tunawa cewa a ranar 21 ga watan Farbariru, 2022, Shugaban ’Yan Sanda na ƙasa, Usman Baba Alkali, ya dauke Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Mamman Dauda, zuwa Jihar Filato.

Shi ma Muhammad Yakubu ba a dade ba aka sauya masa wurin aiki, aka maye gurbinsa da Balarabe Sule a matsayin sabon Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano.

Sai dai ba a je ko’ina ba, shi ma a ranar 8 ga watan Maris, aka sauya shi, bayan korafin cewa shi tsohon Babban Jami’in Tsaro (CSO) na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Bayan nan ne aka tura Faleye Olaleye a matsayin sabon kwamishina, amma ba a kai ko’ina ba, aka janye shi, aka maye gurbin sunansa da Ahmed Kontagora a matsayin wanda zai jagoranci rundunar a lokacin zaben da ke tafe.

A ranar Talata kuma aka sauya Kontagora, aka kawo Usaini Gumel a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

Sai dai Mataimakin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda mai kula da zaben shiyyar Arewa maso Yamma, Hafiz Inuwa, ya bayyana cewa sauye-sauyen kwamishinonin ’yan sandan da aka gani ba abu ne da ya kebanci Jihar Kano ba.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi