• Home  
  • Jigawa na da ƙarfin samar da sama da kashi 50 cikin 100 na buƙatar shinkafar Najeriya – Shugaban NUJ
- Babban Labari

Jigawa na da ƙarfin samar da sama da kashi 50 cikin 100 na buƙatar shinkafar Najeriya – Shugaban NUJ

Shugaban Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), Kwamared Alhassan Yahaya, ya yi kira ga gwamnonin jihohin Najeriya su yi koyi da yadda Gwamnatin Jihar Jigawa ke zuba jari a fannin noma da sauran harkokin samar da arziki, domin magance matsalar ƙarancin abinci da samar da ayyukan yi. Shugaban NUJ ya yi wannan kiran ne a […]

Shugaban Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), Kwamared Alhassan Yahaya, ya yi kira ga gwamnonin jihohin Najeriya su yi koyi da yadda Gwamnatin Jihar Jigawa ke zuba jari a fannin noma da sauran harkokin samar da arziki, domin magance matsalar ƙarancin abinci da samar da ayyukan yi.
Shugaban NUJ ya yi wannan kiran ne a ranar Talata, 11 ga Agusta, 2026, lokacin da ya jagoranci tawagar shugabanni da mambobin ƙungiyar zuwa Jigawa domin duba wasu manyan ayyuka da shirye-shiryen gwamnatin jihar.
Tawagar ta duba cibiyoyin inganta noma ta hanyar amfani da injina, ciki har da taraktoci, injinan girbin amfanin gona da sauran kayan aikin gona, sannan ta ziyarci Fadar Sarkin Dutse tare da duba ayyukan Kamfanin Jigawa State Renewed Hope Technical Services Limited da sauran wurare.
Bayan kammala rangadin, Shugaban NUJ ya ce abin da suka gani a Jigawa ya nuna cewa zuba jari mai yawa a harkar noma na iya taka muhimmiyar rawa wajen samar da isasshen abinci a Najeriya.
Ya bukaci ’yan jarida da sauran masu ruwa da tsaki daga jihohinsu su koma gida da wannan saƙo, su kuma ƙarfafa wa gwamnoninsu gwiwa wajen ƙara zuba jari a harkar noma

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai