Jigawa ta Kulla Babban Yarjejeniya da Gwamnatin Tarayya kan Noman Alfalfa

Gwamnatin Jihar Jigawa ta rattaba hannu kan wata muhimmiyar yarjejeniya da hukumomin tarayya da masu zuba jari domin farawa da noman alfalfa a babban mataki a fadin jihar — wani muhimmin tsiron ciyawar dabbobi da ake amfani da shi wajen kiwo a duniya.
Gwamna Malam Umar Namadi ne ya bayyana haka a Dutse, bayan karɓar tawaga ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar na Hukumar NITDA, Kashifu Inuwa Abdullahi, domin kammala sahihin yarjejeniyar hadin gwiwar.
A cewar gwamnan, aikin zai fara ne da hektare 1,000, kuma yana da damar sauya tsarin kiwon dabbobi a jihar, samar da dubban guraben ayyukan yi da kuma bude sabbin damar fitar da amfanin gona zuwa ƙasashen waje.
Namadi ya ce noma shi ne ginshiƙin tattalin arzikin Jigawa, inda kusan kashi 90 cikin 100 na al’umma ke dogaro da shi, tare da samar da fiye da rabin kudaden shiga na jihar.
“Jigawa tana da zaman lafiya, kuma a bude take ga duk mai son zuba jari. Mun kuduri aniyar inganta harkar noma da kiwo, wannan shiri kuma na daga cikin manyan matakan da za su inganta tattalin arziki,” in ji shi.
Gwamnan ya kara da cewa jihar na shirin fadada noman alfalfa zuwa hektare 100,000, la’akari da nasarar da aka riga aka samu a gonar Matura Farm.
Ya tabbatar da cewa jihar za ta ci gaba da aiki tare da dukkan abokan hulɗa ciki har da NITDA, Bankin NEXIM, MOFI, Jaiz Bank, NSIA da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da nasarar aikin.
Gwamnan ya gode wa masu zuba jari da suka nuna kwarin guiwa ga Jigawa, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta cika nata bangaren na ingiza aikin zuwa nasara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *