Jihar Jigawa na samun babban ci gaba a karatun makarantun firamare, musamman bangaren karatu da lissafi, kamar yadda sabon rahoton 2025 na shirin PLANE da gwamnatin Burtaniya ke daukar nauyi ya nuna.Shirin, wanda ya riga ya kai rabin aikinsa, ya tallafa wa jihar wajen karfafa tsarin ilimi, inda ya kai ga ɗaukar nauyin koyar da sama da dalibai 194,000 a mako 750, tare da horas da malamai 2,522 a kan darussa da tsarin koyarwa a kananan hukumomi bakwai.Sakamakon gwajin da aka gudanar a zangon karatu na 2024/2025 ya nuna cewa yaran makarantun da PLANE ke tallafawa sun fi takwarorinsu a makarantun da ba su cikin shirin fahimtar karatu da lissafi.Inda yara a makarantun PLANE suna iya karanta kalma 13.5 a minti, yayin da wadanda ba sa cikin shirin ke karanta 3.8 kacal.Ko da yake shirin ba ya koyar da Turanci kai tsaye a Jigawa, rahoton ya nuna raguwar yaran da ke a matakin farko na Turanci da kashi 72%, tare da sama da kashi 32% da suka isa matakin fahimtar harshen.Kwamishinan Ilimi na Firamare, Dr. Lawan Yau Danzomo, ya ce an fahimci cewa mai da hankali kan matsalolin tsarin ilimi da gyarawa daga tushe shi ne mafita. Ya bayyana cewa cikin ‘yan shekaru masu zuwa, idan an shimfiɗa shirin ko’ina, “za a ga sakamako mai kyau sosai.”Shugaban Karamar Hukumar Taura, Dr. Shuaib Ibn Hanbali Zarga, ya yaba wa PLANE kan tallafin kayan karatu da inganta koyarwa, yana mai cewa hakan ne ya sa suka sayi littattafai 8,000 da rubutattun littattafai 8,000, tare da ɗaukar karin malamai 125.Shugabannin shirin PLANE sun bayyana cewa Jigawa ta samu sama da kashi 70% a lissafi da kashi 50% a karatu – mafi girma a tarihin shirin a duniya.Rahoton ya kuma nuna muhimmancin sa’ido a makarantu, tallafin al’umma, da samun horo ga malamai, tare da bukatar gwamnati ta ci gaba da: ƙarfafa horaswar malamai, rage karancin malamai da cunkoson aji, dorewar shirye-shiryen bukukuwan karatun hutu, da sabunta tsare-tsaren inganta karatu.Rahoton ya tabbatar da cewa duk da sauran kalubale, Jigawa na kan madaidaiciyar hanya wajen rage gibin karatu a matakin farko da inganta makarantun gwamnati.
2025-12-10
