An kori direban Kamfanin Simintin Mangal bayan jami’an tsaro sun kama shi da motar kamfanin dauke da yara 21 da ake zargin an yi safarar su ne daga jihohin Arewa.
Gwamnatin jihar ta ce yaran da ke tsakanin shekaru 6 zuwa 17 an kama su ne bisa sahihan bayanan sirri.
Sanawar da Kwamishinan Yada labarai na jihar, Kingsley Fanwo, ya fitar bayan kama yaran a cikin motar ta yi zargin za a yi amfani da su wajen horar da ’yan ta’adda.
Kamfanin ya nesanta kansa daga lamarin, ya ce direban ya karya dokokin aiki, kuma ya jefa al’umma cikin haɗari.
- Najeriya Na Rasa Kashi 20 Zuwa 30 Na Kudin Da Take Kashewa Kowace Shekara Saboda Rashin Gaskiya -FIDAC.
- Al’ummar Kururawa da ke Gwarzo, na ci Gaba da Alhini bayan Harin yan Ta’adda
Babban Manajan sashin kula da mulki na kamfanin, Musa Umar, ya ce ba da izininsa direban da aka kama ya fita da motar ba, domin iya jigilar siminta kaɗai suke yi ba ɗaukar fasinja ko yara ba.
Gwamnatin Kogi ta ce za a mika yaran ga gwamnatocin jihohinsu bayan tantancewa, yayin da duk wanda aka samu da hannu a safarar zai fuskanci shari’a bisa dokokin hana safarar yara da kare haƙƙin yara
