Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa, reshen jihar Kano, ta taya zaɓaɓɓen Gwamnan jihar na jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf murnar samun nasara a zaɓen Gwamnan da aka gudanar.
Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Shugaban ƙungiyar Kwamared Abbas Ibrahim, ta tabbatar da cewa Abban zai kai jihar matakin ci gaba ta fuskar ayyukan raya ƙasa da ci gaban al’umma, duba da ƙwarewar da yake da ita da kuma kasancewarsa Injiniya.
Daga ƙarshe kuma ƙungiyar ‘yan jaridun ta yi addu’ar Allah ya yi riƙo da hannun zaɓaɓɓen Gwamnan, kuma ta yi fatan harkar yaɗa labarai ta sami tagomashi a sabuwar gwamnatin.