Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce an samu wasu dake ɗauke da cututtuka a cikin waɗanda ke neman a yi musu auren gata.
Mai magana da yawun hukumar ta Hisbah, Lawan Fagge ya ce an gano wannan ne daga gwaje-gwajen da aka yi kafin auren.
Karanta Wannan: Kano: INEC ta janye ƙarar da ta ɗaukaka kan hukuncin kotu
Malam Lawan Fagge ya ce tuni an maye guraben wadannan mutane da wasu daban. Kuma hukumar Hisbah za ta taimaka wa waɗanda ke ɗauke da cututtukan da magunguna.
Kakakin na Hisbah ya kuma ce sun tantance masu neman aure kusan 5000, gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta aurar da mutane 1800.