Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta janye ƙarar da ta ɗaukaka kan hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamnan Kano ta yanke.
An tabbatar da hakan ne a wata wasiƙa mai ɗauke da sa hannun Suleiman Alƙali, shugaban sashen shari’a na hukumar a Kano.
Suleiman Alƙali ya ce, Hedikwatar hukumar INEC ta umurce shi da cewa a hukumance ba ta da wani dalili na ɗaukaka ƙara kan wannan hukunci.
Shin ya dace INEC ta ɗauki irin wannan mataki a daidai lokacin da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ɗaukaka ƙara? Ina ma’anar hakan ga ɗaukaka ƙarar gwamnan jihar Kano? Ba ita INEC ke da alhakin kare abinda ya faru a shari’ar sauraron ƙarar zaɓen gwamnan jihar nan ba?