Jami’an rundunar yan sanda a jihar Kano sun kama bindigogin AK-47 guda hudu daga wajen wasu miyagu a hanyar Kano zuwa Bauchi.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa dake ɗauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna-Kiyawa, ne ya tabbattar da wannan al’amari jiya.
Inda ya bayyana cewa wata tawaga da ke a babban titi ne suka gano bindigogin a yayin da suke aikin binciken motoci a Kwanar Garko da ke kamar hukumar Garko.
Sanarwar ta ce, an kwato bindigogin ne a lokacin da rundunar ta kama wani direban motar safa da ke kokarin sauya alkibla yayin da daya daga cikin fasinjojin ya sauko rike da wani abin tuhuma.
Inda ya kuma jefar da kayan, ya tsere daga wurin, bayan bincike, an gano wanu buhu dauke da bindigogi kirar AK-47 guda hudu,” in ji shi.
Yayin da rundunar ta ke kara kaimi wajen kamo masu laifuka, ta kuma bukaci mazauna yankin da su ci gaba da kai rahoton faruwar al’amura, wadanda suka yi zargi zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su.