• Home  
  • Kano: Ƙungiyar ‘Yan Jaridu, NUJ, Ta Taya Abba Kabir Yusuf Murna Lashe Zaɓe
- Labarai

Kano: Ƙungiyar ‘Yan Jaridu, NUJ, Ta Taya Abba Kabir Yusuf Murna Lashe Zaɓe

Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa, reshen jihar Kano, ta taya zaɓaɓɓen Gwamnan jihar na jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf murnar samun nasara a zaɓen Gwamnan da aka gudanar.

Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa, reshen jihar Kano, ta taya zaɓaɓɓen Gwamnan jihar na jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf murnar samun nasara a zaɓen Gwamnan da aka gudanar.

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Shugaban ƙungiyar Kwamared Abbas Ibrahim, ta tabbatar da cewa Abban zai kai jihar matakin ci gaba ta fuskar ayyukan raya ƙasa da ci gaban al’umma, duba da ƙwarewar da yake da ita da kuma kasancewarsa Injiniya.

Daga ƙarshe kuma ƙungiyar ‘yan jaridun ta yi addu’ar Allah ya yi riƙo da hannun zaɓaɓɓen Gwamnan, kuma ta yi fatan harkar yaɗa labarai  ta sami tagomashi a sabuwar gwamnatin.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000