• Home  
  • Kashim Shettima ya isa Bauchi halartar jana’izar Sheikh Ɗahiru Bauchi
- Babban Labari - Labarai

Kashim Shettima ya isa Bauchi halartar jana’izar Sheikh Ɗahiru Bauchi

Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya isa jihar Bauchi domin halartar janaizar fitaccen malamin addinin nan da ya rasu a jiya Alhamis, Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Mataimakin shugaban ƙasar ya sami tarba ne daga gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad da kuma na jihar Neja Umar Bago wanda tuni shi ma ya isa jihar. Ana sa […]

Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya isa jihar Bauchi domin halartar janaizar fitaccen malamin addinin nan da ya rasu a jiya Alhamis, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Mataimakin shugaban ƙasar ya sami tarba ne daga gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad da kuma na jihar Neja Umar Bago wanda tuni shi ma ya isa jihar.

Ana sa ran nan gaba kaɗan ne za a yi jana’izar marigayin a wani filin idi da ke jihar Bauchi, kafin a kai shi makwancinsa da ke babban massalacinsa.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000