Kasar Saudiya ta kaddamar da wani shiri na musamman na dashen na’urar ji ( Cochlear implant) wadda zata taimaka wa mutane da suke fama da matsalar kunne.
Cibiyar agajin jin kai da tallafi ta sarki Salman na Saudiya KSRELIEF, ta dauki nauyin shirin yin tiyatar ga yara yan Nijeriya guda 30, wanda aka gudanar a birnin tarayya Abuja.
Cochlear implant wata na’ura ce ta musamman da ake dasawa cikin kunne ta hanyar yin tiyata, domin ta taimaka wa mutanen masu fama da rashin ji, don magance matsalar a fadin Nijeriya.
Shirin dashen hadin gwiwa ne da gwamnatin Nijeriya karkashin ma’aikatar lafiya, inda za a yi wa yara 30 da nufin dawo musu da jin magana kamar sauran al’umma .
Shirin tiyatar ya kunshi kulawa daga farko har karshe, ciki har da bincike (diagnosis), tiyata, bibiyar marasa lafiya da koyan sauraro, da kuma koyan magana.
Wannan mataki ne da zai sauya rayuwar wadanda za su amfana da kuma iyalansu baki daya.
Wakilin jakadancin kasar Saudiyya a Nijeriya na Wucin-gadi, Malam Sa’ad bin Fahd Al-Marri, ya yaba da hadin gwiwar, tare da jaddada muhimmancin jin kai na wannan aiki.
- Yan Sanda Sun Kama Fasto Cikin Gungun Mutanen Da Ake Zargi Da Satar Yara Da Siyarwa.
- EFCC Ta Gayyaci Tsohon Ministan Sharia Abubakar Malami
Ya ce wannan shiri ya nuna yadda masarautar Saudiyya ta kuduri aniyar tallafa wa al’umma masu bukata da kuma karfafa tsarin kiwon lafiya a kasashen waje.
Ya kara da cwa sun kuduri aniyar samar da hanyoyin magance matsaloli na gaskiya da kuma kara dankon zumunci tsakanin Saudiyya da Nijeriya,Shirin dashen na’urar ji na daga cikin jerin ayyukan jin kai da KSRelief ke ci gaba da aiwatarwa a Nijeriya da ma kasashen Afirka baki daya, inda cibiyar ke tallafa wa aiyukan lafiya da yaki da cututtuka, da kuma taimakon gaggawa ga al’ummomin da ke fama da rikice-rikice.
Haka kuma, shirin ya kara tabbatar da kudurin Masarautar Saudiyya karkashin jagorancin Sarki Salman bin Abdulaziz, na habaka muhimman aiyukan lafiya da kuma mika tallafin jin kai ga al’ummomin masu bukatar taimako a fadin dunya.
