• Home  
  • Kotu ta ɗage shari’ar shugabancin jam’iyyar ADC har sai baba ta gani
- Babban Labari

Kotu ta ɗage shari’ar shugabancin jam’iyyar ADC har sai baba ta gani

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ɗage shari’ar da Nafi’u Bala Gombe ya shigar inda yake ƙalubalantar shugabancin jam’iyyar ADC tsagin tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya David Mark, har illa masha Allah. Mai shari’a Emeka Nwite ne ya ɗage shari’ar bayan wanda ya shigar da ƙarar ya buƙaci a canza masa alƙalin da ke […]

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ɗage shari’ar da Nafi’u Bala Gombe ya shigar inda yake ƙalubalantar shugabancin jam’iyyar ADC tsagin tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya David Mark, har illa masha Allah.

Mai shari’a Emeka Nwite ne ya ɗage shari’ar bayan wanda ya shigar da ƙarar ya buƙaci a canza masa alƙalin da ke sauraron shari’ar.

Ɗaya daga cikin lauyoyin jam’iyar ADC DR Sulaiman Usman ya ce lamarin ya zo musu da bazata ganin cewa ɓangaren Nafi’u Bala ne suka shigar a ƙarar, sai kuma yanzu gashi su ke da ƙasa a gwiwa har suke nema a tura ta wata kotu, wanda kuma yin hakan zai sa shari’ar ta koma ƙasa.

A cewar sa kawai suna neman a kai su kotun da za ta yi musu abinda suke so ne ko abin da zai musu dadi, kuma a cewar sa ‘hakan bai dace ba a shari’a’.

Lauyan ya kuma ce za su mayar da martani ta hanyar rubutu ga babban alkali kan cewa babu hujjar da za ta sa a ɗauke shari’ar.

“ Babu wani abu da ya faru a shari’ar da wani zai kawo koke, sannan har kotun koli ta yabi alkalin saboda babu wani abu da ya taɓa yi na tauye wa wani haƙƙi ko nuna ɓangaranci ko rashin adalci’’. In ji lauyan.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000