Rundunar ƴan sandan jihar Kadun,a ta gurfanar da mutane 24 a gaban kotun majistare mai lamba huɗu bisa zarginsu da hannu a kisan wata malamar Islamiyya mai suna Ummulkhairi a yankin Mararrabar Jos da ke jihar Kaduna.
Ana tuhumar mutanen da laifin haɗa baki da tayar da tarzoma da ɓarnata dukiyar jama’a da ta ƴan sanda da kuma kisan kai.
Hukumomin tsaro sun bayyana cewa wasu fusatattun mutane suka farmaki matar tare da kashe ta da kuma ƙona gawarta, bayan zargin cewa mai satar yara ce.
Mai shari’a,Naheed Ibrahim Abdul, ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 21 ga watan Yulin 2026 domin karɓar shawarwari daga ma’aikatar Shari’a ta Jihar kafin gurfana da su a kotun da take da hurimi.
Lauyan rundunar ƴan sandan jihar, CSP Martins Danjuma, ya bayyana cewa zargin da aka yi wa marigayiyar ba shi da wani tushe, yana mai cewa matar tana tambayar hanyar zuwa wani taro ne lokacin da wasu mutane suka fermata, kuma jami’an ƴan sanda da sojoji sun yi bakin ƙoƙarinsu domin tseratar da ita har sai da jiwa wasu ƴan sanda raunuka kafin su kashe ta.
Ya ƙara da cewa an kama sama da mutane 100 dangane da lamarin, kuma ana ci gaba da tantance su domin tabbatar da an gurfanar da duk wanda ke da hannu a aikata laifin.
A nasa ɓangaren, lauya mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam, Barista Usman Salisu, ya ce sun shiga cikin shari’ar ne domin tabbatar da an yi wa iyalan marigayiyar adalci.
Yanzu haka dai mutane 24 ne aka fara gurfanarwa cikin waɗanda aka kama bisa zargin hannu a kisan kan Ummulkhairi a yankin Mararrabar Jos da ke jihar Kaduna.

