• Home  
  • Kotu Ta Aike Da Dan TikTok Din Da Ke Wanka A Kan Titi A Kano Gidan Yari
- Babban Labari - Labarai

Kotu Ta Aike Da Dan TikTok Din Da Ke Wanka A Kan Titi A Kano Gidan Yari

Wata kotun Majistare da ke zamanta a unguwar Nomansland a Kano ta tura wani matashin dan TikTok din nan da ya yi kaurin suna wajen tare titi yana wanka a Kano gidan kurkuku. Kotun dai ta sami matashin mai suna Umar Hisham Fagge, wanda aka fi sani da Tsulange, zuwa gidan yari har zuwa ranar […]

Wata kotun Majistare da ke zamanta a unguwar Nomansland a Kano ta tura wani matashin dan TikTok din nan da ya yi kaurin suna wajen tare titi yana wanka a Kano gidan kurkuku.

Kotun dai ta sami matashin mai suna Umar Hisham Fagge, wanda aka fi sani da Tsulange, zuwa gidan yari har zuwa ranar 3 ga watan Yulin 2025.

Kotu, wacce ke karkashin Mai Shari’a Hadiza Muhammad Hassan, ta yanke hukuncin ne ranar Alhamis.

Hukumar Tace Fina-finai ta jihar Kano ce dai ta gurfanar da Tsulange a gaban kotun biyo bayan kama shi da laifin sanya rigar ciki ta mata da kuma tare titi yana yin wanka tare da bidiyon barkwanci, in ji mai magana da yawun hukumar, abdullahi Sani Sulaiman.

Hukumar ta ce hakan ya saɓa wa al’adar bahaushe da tarbiyyar addinin musulunci.

Tuni kotun ta tura matashin gidan gyaran hali, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike da kuma samun damar duba matakin ladabtarwa na gaba.

Hukumar ta kuma ce za ta ci gaba da dauka irin wannan mataki domin kawo karshen aikin rashin da’a a kafafen sada zumunta na zamani ga masu amfani da su a jihar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000