650
Daga : Sharif Khalifa Sharifai
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf , bayan dawowar sa daga kasa mai tsarki, ya kai ziyara kasuwar wayoyi ta Farm center domin jajantawa wadan Iftila`in Gobara ya rutsa ya shafa.
Gwamnan ya kai ziyarar ne da yammacin ranar Juma`a ya kuma samu rakiyar sakataran Gwamanatin jihar, Umar Faruk , shugaban karamar hukumar Tarauni.
A jawabinsa mai girma Gwamna yaja hankalin yan kasuwar da su kasance ma su kula da abinda ya shafi harkar wutar lantarki.
Abba Kabir ya yi mu su alkawarin gyara shagunan da suka kone sannan zai sake gina wasu Shaguna a cikin kasuwar .
Ya kara da cewa za a samar wa da yan kasuwar ofishin agajin gaggawa na kashe gobara ( Fire Service ) a cikin kasuwar .