• Home  
  • Gwamna Uba Sani Ya Kaddamar Da Cibiyar Koyar Da Sana’o’i Da Asibitin Kwararru A Kaduna
- Babban Labari - Labarai

Gwamna Uba Sani Ya Kaddamar Da Cibiyar Koyar Da Sana’o’i Da Asibitin Kwararru A Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya kaddamar da aiyukan da samar domin ci gaban al’ummarsa wanda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci kaddamar da su a ranar Alhamis a jihar. Gwamna Uba Sani ya yi wadannan aiyuka ne cikin shekaru biyu da ya yi yana mulkin jihar. Wasu daga cikin ayyukan da aka […]

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya kaddamar da aiyukan da samar domin ci gaban al’ummarsa wanda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci kaddamar da su a ranar Alhamis a jihar.

Gwamna Uba Sani ya yi wadannan aiyuka ne cikin shekaru biyu da ya yi yana mulkin jihar.

Wasu daga cikin ayyukan da aka ƙaddamar sun haɗa da asibitin ƙwararru mai gadaje 300 da gwamnatin jihar ta gina don bunƙasa harkokin lafiya da cibiyar koyar da sana’o’i, da kuma motocin sufuri masu amfani da iskar gas ta CNG guda 100.

A cikin waɗanda suka yi wa Shugaba Tinubu rakiya sun haɗa da mataikamin Shugaban ƙasa na musamman kan harkokin siyasa, Sanata Ibrahim Masari, da mai taimaka wa shugaban kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu da Shugaban Majalisar Wakilai,  Tajudeen Abbas da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau I. Jibrin da wasu manyan jami’an gwamnati.

Kazalika, Bola Tinubu ya kuma buɗe hanyar Kafanchan da Tudun Biri da Kauru zuwa Pambegua.   
Haka kuma shugaban ya samu tarba daga gwamnan jihar Kaduna tare da takwarorinsa na makwabtan jihohi, Ziyarar Tinubun na zuwa ne kwana guda bayan ziyarar jaje da ya kai jihar Benue da ke fama da rikice-rikice.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai