Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe da ke yanke hukunci kan karar da jam’iyyar APC ta shigar gabanta tana mai ƙalubalantar nasarar da Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya samu ta bayyana matsayarta.
Kotun ta ayyana Dr. Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓen ranar 18 ga watan Maris na wannan shekaru.
Kotun mai alƙalai guda uku, ta ba wa INEC umarnin janye shaidar da ta ba wa Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan Kano.
Kotun ta kwashe ƙur’u dubu ɗari shida da biyar da ɗari shida da sittin da uku daga ƙuri’un da Abba ya samu a matsayin waɗanda ba su da inganci saboda ba a yi musu stamfi ba da sa-hannu.
Wannan na zuwa ne bayan shafe kusan watanni shida da ayyana Abba a matsayin gwamnan Kano wanda aka rawaito Gawuna na bayyana karɓar faɗuwar da ya yi a zaɓen.