Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya yi watsai da ayyana Dakta Jamilu Isyaku Gwamna da Jam’iyyar APC ta yi a matsayin dan takararta na Gwamnan Jihar Gombe a zaben shekarar 2027.
Pantami wanda ke neman takarar kujerar gwamnan jihar a APC, ya bayyana shirinsa zuwa kotu domin kalubalantar abin da ya kira dauki-dora, wanda bai samu halarta ko amincewar sauran masu neman takarar ba.
Ya bayyana cewa abin da aka yi da sunan sulhun ya saba wa ka’ida da tsarin mulki da kuma adalci, hasali ma, shi yana Abuja ya samu labarin nadin Jamilu. Ya yi kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu su zama masu bin doka da oda.
Shugabannin Jam’iyyar APC na jihar sun cimma matsayar amincewa da takarar Jamilu isiyaku Gwamna ne a taron da aka gudanar a ranar Lahadi, domin a fitar da ’yan takara cikin hadin kai domin karfafa damar jam’iyyar a zabe mai zuwa.
A yayin taron ne aka bayyana Jamilu Ishiaku Gwamna a matsayin zabin bai daya, wasu daga cikin masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa an dauki matakikn ne domin kauce wa rikice-rikicen cikin gida da kuma tabbatar da hadin kan jam’iyyar.
Sai dai Pantami, wanda yake cikin masu neman takarar kujerar gwamna a Jam’iyyar APC a Jihar Gombe, ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda aka bi wajen cimma wannan matsaya, yana mai cewa bai dace a hana sauran masu sha’awar takara damar fafatawa ba.
a wata sanarwa da ya fitar, Pantami ya ce ba da yawunsu aka zabi Jamilu Gwamna ba, hasali ma ba da su aka yi zaman ba, yana mai cewa ya kamata a ba wa kowane mai neman kujerar damar halartar zaman sannan a nemi amincewarsa.
Ya jaddada cewa tsarin dimokuradiyya na bukatar a bai wa kowa dama ya gwada karfinsa ta hanyar zabe na gaskiya da adalci, maimakon yin karfa-karfa ga ga ’yan jam’iyya.
Tsohon ministan ya kuma ya kari da cewa duk da cewa dokar zabe ta amince da yin sulhu a tsakanin ’yan takara, idan aka samu mutum daya da ya ki amince, ya zama dole a yi zaben fid-da-gwani.
Pantami ya kuma yi gargadin cewa irin wannan tsari na iya haifar da rabuwar kai a cikin jam’iyyar, musamman idan aka yi watsi da ra’ayoyin wasu daga cikin mambobinta.
“Ya kamata a yi adalci ga kowa tare da bin ka’idojin jam’iyya domin a samu karbuwa daga dukkan bangarori,” in ji shi.
Sai dai Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Gombe, Muhammad Dantata Ndus, sun kare matakin da aka dauka, suna masu cewa tsarin fidda dan takara ta hanyar sulhu ba sabon abu ba ne a APC, kuma yana taimakawa wajen rage sabani da gasa mai zafi a tsakanin ’yan takara.
Sun kara da cewa manufar hakan ita ce a hada kan jam’iyya domin tunkarar babban zabe cikin karfi da tsari.
Duk da haka, lamarin ya jawo muhawara mai zafi a tsakanin magoya bayan jam’iyyar a jihar, inda wasu ke goyon bayan tsarin sulhu, yayin da wasu ke ganin ya kamata a bar kowa ya fafata domin tabbatar da adalci da gaskiya.
Masu sa ido kan harkokin siyasa sun ce yadda jam’iyyar za ta tafiyar da wannan sabani na da matukar muhimmanci, domin zai iya shafar hadin kanta da kuma nasararta a zaben 2027.
A halin yanzu, ana sa ran za a ci gaba da tattaunawa a cikin jam’iyyar domin lalubo hanyar da za ta kawo maslaha tare da tabbatar da hadin kai tsakanin ’ya’yanta.
