Kotun sauraron kararrakin zabe ta ayyana ranar Laraba, 20 ga watan Satumba domin yanke hukuncin shari’ar kan kujerar Gwamnan Kano.
A cikin wata sanarwa da ta fito daga Kotu sauraren kararrakin zaben Mai dauke da sa hannun maga takardar kotun, ta ce za a gudanar da zaman yanke hukuncin ne a babbar Kotun jihar Kano dake Miller Road a Kano.