Kotu ta yanke wa Mai Kayan Miya hukuncin kisa tare da wanke abokinsa a Kano

Babbar kotun jihar Kano, mai lamba 24 da ke zaman ta a unguwar Bompai, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Aisha Mahmoud, ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wani mutum da aka samu da laifin haɗa baki da garkuwa, da kuma laifin kisan kai.

Gwamnatin jahar Kano ce, dai ta gurfanar da mutanen da suka hadar da Abdul-Aziz Adamu mai kayan miya, da kuma Abdullahi Alasan Ɗan mama, inda ake zargin su da laifin haɗa baki suna sace mutane domin biyan kudin fansa, an kuma zargin cewar, sun kashe wasu mutane waɗanda aka samu gawarwakinsu a gidan mai kayan miyan da ke ƙaramar hukumar Dawakin kudu.

Da take bayyana matsayar kotun, a ranar Alhamis 11 ga watan Disamba, 2025, mai shari’a A’isha Mahmoud, ta ayyana cewar, kotun ta gamsu da shaidun masu gabatar da ƙara akan wanda ake tuhuma na farko, a don haka ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Mutum na biyun da ake tuhuma, kotun ta wanke shi ta kuma sallame shi nan take.

An dai sha neman mutanen da suka ɓata a ƙaramar hukumar Dawakin kudu, sai daga ƙarshe a ka samu gawarwakin wasu mutanen a gidan mai kayan miyan, lamarin da ya tayar da hankalin al’umma a lokacin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *