• Home  
  • An kai hari gidan jami’in ɗan sanda a Yobe
- Babban Labari - Labarai

An kai hari gidan jami’in ɗan sanda a Yobe

Wasu mahara da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun kai hari gidan babban Jami’in kula da ofishin ‘yan sandan na Tattaɓa, ASP Mohammed Modu, da ke yankin Bara a ƙaramar hukumar Gulani, Jihar Yobe. Kamar yadda rahoton Jami’an tsaro ke nunawa cewa, da misalin ƙarfe 1:30 na tsakar daren ranar 9 ga Disamba, maharan […]

Rundunar 'yan sanda na shirin janye jami'anta masu yi wa manyan mutane rakiya da tsaro

Wasu mahara da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun kai hari gidan babban Jami’in kula da ofishin ‘yan sandan na Tattaɓa, ASP Mohammed Modu, da ke yankin Bara a ƙaramar hukumar Gulani, Jihar Yobe.

Kamar yadda rahoton Jami’an tsaro ke nunawa cewa, da misalin ƙarfe 1:30 na tsakar daren ranar 9 ga Disamba, maharan suka mamaye gidaje uku na jami’in, suka sace babur ɗinsa na Haojue da kekuna uku da mota ƙirar Golf 3, da sauran kayansa kafin su ƙona gidaje uku da motar Honda Civic.

An yi zargin cewa, wani mai kai rahoto ne ga ‘yan ƙungiyar da ke cikin al’ummar wannan yankin ya bada rahoton Jami’in ga waɗannan maharan.

Jami’an tsaro sun ziyarci wurin da lamarin ya faru kuma sun tattara bayanai game da ɓarnar, ba tare da an samu rahoton asarar rayuka ba.

An shawarci jami’in da ya yi taka-tsantsan yayin da ake ƙara tsaurara sa ido da sintiri a yankin don hana sake kai hari a yankin.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai