• Home  
  • Kotun Koli ta soke afuwar Maryam Sanda, ta sake tabbatar mata da hukuncin kisa.
- Babban Labari - Labarai

Kotun Koli ta soke afuwar Maryam Sanda, ta sake tabbatar mata da hukuncin kisa.

Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin kisa kan Maryam Sanda bisa samunta da laifin kashe mijinta Bilyaminun Bello. Alƙalan kotun guda huɗu a cikin biyar ne suka tabbatar hukuncin, inda ake yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan watsi da ɗaukaka ƙararta, kamar yadda mai shari’a Moore Adumein ne ya sanar da hukuncin […]

Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin kisa kan Maryam Sanda bisa samunta da laifin kashe mijinta Bilyaminun Bello.

Alƙalan kotun guda huɗu a cikin biyar ne suka tabbatar hukuncin, inda ake yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan watsi da ɗaukaka ƙararta, kamar yadda mai shari’a Moore Adumein ne ya sanar da hukuncin a madadin sauran alƙalan.

 

 

Kotun ta ce Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi rangwame ga Maryam alhalin ana ci gaba da sauraron shari’arta a gaban kotun ɗaukaka ƙara, kamar yadda tashar Channles ta ruwaito.

A ranar 27 ga watan Janairun 2020 ne kotu a Abuja ta yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunta da laifin da kashe mijinta Bilyaminu Bello a gidansu na Abuja shekarar 2017.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai