Wasu Yan Nijeriya Sun Roki Hukumar PSC Ta Yi Adalci Wajen Daukar Sabbin Yan Sanda Dubu 50

Wasu yan Nijeriya sun yi kira ga hukumar kula da aiyukan yan sandan Nijeriya ta yi adalci wajen diban sabbin jami’an yan sanda, a dukkan matakan da ake da bukata.

Kiran na su na zuwa kwana guda bayan hukumar kula da aiyukan yan sandan (PSC) ta sanar da bude Shirin fara daukar yan sandan dubu 50 don karfafa tsaron cikin gida.

A cewar wasu daga cikin wadanda gidan Telebijin da Radiyo na MUHASA na ya zanta dasu , sun bayyana takacinsu kan yadda cusa wadanda basu dace ba yayin tantancewar.

Haka zalika wata matashiya da take da sha’awar shiga aikin ta bayyana damuwarta, kan rashin samun goyon baya da kuma karfafa musu gwiwa, daga wajen iyaye wanda hakan ke yi musu tarnakin shigar harkar tsaro.Hukumar kula da aiyukan yan sandan ta ce dukkan masu neman shiga wajibi ne su kasance suna da takardun kammala makarantun sakandare na GCE, SSCE/NECO ko makamantansu da  aƙalla nasara a darussa biyar ciki har da Turanci da Lissafi.

Ga rahotan Mujahid Wada Musa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *