A ci gaban da zaman kotun sauraren ƙararraki na zaɓen shugaban ƙasa, kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasar ta caccaki dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, kan rashin shirya wa karar da ya shigar na kalubalantar nasarar Shugaba Bola Tinubu
Ɗaya daga cikin manyan lauyoyin da ke cikin tawagar lauyoyin masu shigar da karar, Emeka Okpoko, ya nemi gabatar da takardun zabe a matsayin shaida a gaban kotu.
Sai dai bayan gabatar da takardun, kotu ta ce ba a gabatar tare da shirya takardun yadda ya kamata ba kuma ba.
Don haka kotun ta dage sauraron karar na tsawon mintuna 10 sannan ta bukaci tawagar lauyoyin da su sake gabatar da takardun kamar yadda yakamata.
Duk da haka, bayan dawowa daga hutun, tawagar lauyoyin sun gaza gabatar da takardun cikin tsari.
Inda kuma kwamitin alƙalan mai mambobi biyar ya a karkashin jagorancin Haruna Tsammani, ya shawarci masu shigar da karar da su nemi a ɗage zamansu domin su tsara takardunsu yadda ya kamata.
Da yake mayar da martani, Awa Kalu, wani babban lauya a tawagar masu shigar da karar, ya ce ba za su karɓi shawarar dage zaman ba, sai dai za su mika shaidun kananan hukumomi 16 da ke kasa.
Zuwa yanzu dai Jihohi shida Jam’iyyar Labour ta iya gabatar da takardun shaidun zaɓukansu.
A ƙarshe dai an ɗage sauraron karar har zuwa ranar 2 ga watan Yuni.