Kotun Ƙolin Najeriya ta sanya ranar 22 ga watan Afrilu domin sauraron daukaka kara da ta samo asali daga rikicin shugabanci da ke addabar jam’iyyar PDP.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa ƙararrakin sun fito ne daga wani ɓangare na jam’iyyar karkashin jagorancin tsohon Ministan Ayyuka na Musamman, Kabiru Tanimu Turaki, wanda ke ƙalubalantar hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da aka yanke a ranar 9 ga Maris.
Kwamitin alkalai biyar na Kotun Ƙoli, karkashin jagorancin Mai shari’a Mohammed Garba, ne ya tsayar da ranar a ranar Talata bayan amincewa da buƙatar a gaggauta sauraron shari’ar.
Kotun ta kuma rage wa’adin da aka bai wa ɓangarorin domin gabatar da takardunsu, inda ta umarci waɗanda ake ƙara su gabatar da martaninsu cikin kwanaki biyar, yayin da masu ɗaukaka ƙara suka samu kwanaki biyu domin mayar da martani idan akwai.
Ƙarar ta samo asali ne daga hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara wanda ya tabbatar da hukuncin Kotun Tarayya da ke Abuja, wadda ta hana PDP gudanar da babban taronta na ƙasa har sai ta bi tanade-tanaden doka, ciki har da Dokar Zaɓe da kuma ƙa’idojin jam’iyyar.
Alkalai James Omotosho da Peter Lifu ne suka yanke hukuncin Kotun Tarayya bayan wasu mambobin jam’iyyar da suka nuna rashin gamsuwa, ciki har da tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido, sun shigar da ƙara.
A zaman kotun na ranar Talata, manyan ‘yan siyasa sun halarci shari’ar, ciki har da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, tare da Turaki da sauran jiga-jigan jam’iyyar.

