Kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC) ta ce za su yi tattaunawa kan sabon tsarin mafi karancin albashi zuwa N100,000 ko N200,000 saboda tsadar rayuwa.
A yayin da kungiyar kwadago da kuma TUC suka shirya fara yajin aiki a jiya Talata, sakamakon tasirin cire tallafin man fetur, sun janye yajin aikin ne bayan wata ganawar da suka yi da hukumomin gwamnati a Abuja da yammacin ranar Litinin.
Sai dai a cewar shugaban kungiyar ta NLC, Joe Ajaero, sun dauki matakin ne domin bai wa gwamnati lokaci ta cika wani bangare na yarjejeniyar da aka cimma da kungiyoyin kwadago, inda ya kara da cewa bayar da karin albashin Naira dubu 35 ba sabon abu bane. Mafi karancin albashin da ya ce a bai wa ma’aikata zai iya kaiwa N200,000.