Kungiyar Kwadago ta ƙasa reshen jihar Kano ta magantu kan matsalar Ma’aikata akalla 10,000 da gwamnatin jihar Kano ta tsayar musu albashi.
Idan za’a iya tunawa, a ƴan kwanakin baya ne, gwamnan jihar Kano, engr. Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin tsayar da albashin ma’aikata da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya dauka.
Shugaban kungiyar na jihar kano, Kabiru Inuwa ya bayyana cewa za su gudanar da wata ganawa don samo mafita a kan matsalar.
Shugaban ya bayyana cewar za su samo mafita a kan wanna matsala a ganawar da za su yi a ranar Litinin.
Haka kuma a yayin tattaunawar, wadanda abin ya shafa za su rubuto matsalolinsu ga kungiya don nemo mafita.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce sun dakatar da biyan albashin ma’aikatan har sai lokacin da aka gama tantance su.