• Home  
  • Kwalejin Fasaha ta Kogi ta dakatar da lakcarori 7 kan cin zarafin ɗalibai
- Labarai

Kwalejin Fasaha ta Kogi ta dakatar da lakcarori 7 kan cin zarafin ɗalibai

Hukumar gudanarwar Kwalejin Fasaha ta Jihar Kogi ta dakatar da wasu lakcarori bakwai bisa zargin cin zarafin ɗalibai ta hanyar neman lalata da kuma sayar da handout da littattafai ba bisa ƙa’ida ba. Jami’in Hulɗa da Jama’a na kwalejin, John Onimisi, ya tabbatar da matakin, yana mai cewa an kafa kwamitin bincike domin gano gaskiyar […]

Hukumar gudanarwar Kwalejin Fasaha ta Jihar Kogi ta dakatar da wasu lakcarori bakwai bisa zargin cin zarafin ɗalibai ta hanyar neman lalata da kuma sayar da handout da littattafai ba bisa ƙa’ida ba.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na kwalejin, John Onimisi, ya tabbatar da matakin, yana mai cewa an kafa kwamitin bincike domin gano gaskiyar zarge-zargen.
Shida daga cikin malaman an dakatar da su ne kan zargin tilasta wa ɗalibai sayen takardun handout da littattafai, yayin da aka dakatar da ɗaya bisa zargin neman lalata da wata ɗaliba.

Wasu ɗalibai mata sun yi zargin cewa wasu malamai na neman kuɗi ko lalata da su domin ba su maki ko kuma su tsallake jarabawa.

Haka kuma sun yi zargin cewa an fara sake samun matsalolin ƙungiyoyin asiri da wasu munanan ɗabi’u a harabar makarantar.

Sai dai hukumar makarantar ta ce tuni ta fara ɗaukar matakan ladabtarwa, tare da tabbatar da cewa za ta fitar da sakamakon binciken da zarar an kammala shi.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000