Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya ce yana da ƙwarewa da salon shugabancin da za su ba shi damar haɗa kan Najeriya idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa.
Obi ya bayyana haka ne a shirin siyasa na gidan talabijin na Channels a daren ranar Lahadi.
Obi, ya kuma musanta zargin cewa zai raba kan ƙasar idan ya zama shugaban ƙasa.
Ya ce ayyukan da ya yi a baya sun nuna cewa ya himmatu wajen haɗa kan ’yan Najeriya.
Obi, ya ce ya kai ziyara zuwa jihohi da dama a Arewacin Najeriya domin tallafa wa al’ummomin da rikice-rikice da iftila’i suka shafa.
Ya bayyana yadda ya je Jihar Borno domin jajanta wa tsohon gwamnan jihar, Ali Modu Sheriff bayan Boko Haram ta kashe ɗan uwansa.
Haka kuma ya ce ya bayar da gudummawar Naira miliyan 50 sakamakon ambaliyar ruwa da ta auku a jihar tare da ziyartar sansanonin ’yan gudun hijira.
Ya kuma ce ya taimaka wajen haƙa rijiyoyin burtsatse, da tallafa wa makarantu, asibitoci da sauran ayyukan ci gaba a jihohin Kano, Kaduna, Gombe, Bauchi da Sakkwato.
Obi, ya ce idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa, gwamnatinsa za ta yi aiki wajen haɗa kan ƙasa, samar da zaman lafiya da kuma bai wa kowane ɗan Najeriya dama iri ɗaya ba tare da la’akari da ƙabilanci ko addini ba.
Ya kuma musanta zargin cewa ya taɓa yin kalaman da ke nuna wariya ga mutanen Arewa, inda ya tabbatar da cewar waɗannan kalamai ba gaskiya ba ne.
Ya ƙara da cewa tattaunawar siyasa ya kamata ta fi mayar da hankali kan matsalolin tsaro, talauci, ilimi da kiwon lafiya maimakon sukar mutanen da ke adawa da gwamnati mai ci.

