Kwamishinan yan sandan kihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya karɓi bakuncin Kwamandan kwalejin sojan ruwa ta Nijeriya da ke Dawakin-Tofa, Commodore Ahmad Abubakar Madawaki, a hedikwatar rundunar da ke Bompai, Kano.
Kwamandan ya ce ya je rundunar ne domin ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin rundunar sojan ruwa da yan sandan Kano, musamman wajen horas da jami’an da gudanar da aikin haɗin gwiwa.
Ya yaba da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin hukumomin biyu, yana mai cewa haɗin gwiwar na taimakawa wajen yaƙi da miyagun laifuka da kuma tabbatar da tsaron al’umma.
Yayin da zaɓuka ke gabatowa, Commodore Madawaki ya tabbatar wa CP Bakori cewa Kwalejin Sojan Ruwa za ta ba da cikakken goyon baya wajen tabbatar da an gudanar da zaɓe cikin lumana da gaskiya a jihar.
A nasa jawabin, CP Bakori ya bayyana jin daɗinsa kan irin haɗin gwiwar da ke tsakanin hukumomin tsaro a Kano, yana mai cewa hakan ya samo asali ne daga kyakkyawar fahimtar juna da shugabannin hukumomin ke yi.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa rundunar yan sandan Kano ta fara horas da jami’ai tare da sake horas da wasu, domin shirye-shiryen tunkarar zaɓukan da ke tafe.
Ya buƙaci Kwalejin Sojan Ruwa da sauran hukumomin tsaro su ƙara yin irin wannan shiri, domin tabbatar da ingantaccen aikin haɗin gwiwa kafin da kuma lokacin zaɓe.
Rundunar yan sandan Jihar Kano ta ce za ta ci gaba da haɗa hannu da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron al’umma a faɗin jihar.
