Hukumar kwastam ta Najeriya ta kama harsasai 3,300 da wasu kayayyakin fasa-ƙwauri da darajarsu ta kai Naira miliyan 365.1 a iyakar Seme.
Daga cikin kayayyakin akwai tabar wiwi, magunguna, sigari 310,000, da motoci daban-daban.
Haka kuma, jami’an sun kama wata mota da aka bayyana cewa tana ɗauke da kayan abinci, amma aka gano buhunan noodles 1,306 da suka lalace.
An miƙa harsasan da wani wanda ake zargi ga yan sanda domin bincike, yayin da kwastam ta ce za ta ƙara ƙarfafa sa ido domin dakile safarar makamai, miyagun ƙwayoyi da sauran kayayyakin aka haramta.
