Kwamishinan ƴan sandan Jihar Kano, tare da wakilan sauran hukumomin tsaro, sun halarci bikin tunawa da jaruman sojojin Najeriya, wanda aka gudanar a garin Dotsa, da ke kan hanyar Zariya, a Ƙaramar Hukumar Kumbotso.
Ana gudanar da wannan biki ne a ranar 15 ga watan Janairu na kowace shekara, domin tunawa da gudunmawar da sojoji suka bayar wurin cigaban ƙasa.
Haka kuma, ana amfani da wannan rana wajen jajantawa juna bisa yawan sojojin da ƙasar ke ci gaba da rasawa a fagen fama, a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar manyan ƙalubalen tsaro a sassa daban-daban na ƙasar, musamman a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.
Duk da irin wannan sadaukarwa, har yanzu wasu tsofaffin sojoji da iyalan jaruman da suka rasa rayukansu na ci gaba da korafi kan rashin isasshen kulawa, bayan sun sadaukar da kansu domin kare martabar Najeriya.