Ƙaramin Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Dr Tunji Alausa, ya ce gwamnnatin tarayya na kan haɗa guiwa da kamfanonin haɗa magunguna domin rage tsadar da magungunan cutar kansa ke yi da ma tsarin ba da kulawa a ƙasar nan.
Ministan ya bayyana hakan ne a yayin taron Ranar Masu Fama da Cutar Kansa ta Duniya mai taken, “Matsalar Tattalin Arziƙi Da Haraji Da Kula Da Yadda Ficewar Kamfanonin Haɗa Magunguna Daga Najeriya Ya Ke Shafar Kula Da Da Cutar Kansa”.
Ya kuma ce a yanzu haka, gwmnatin ƙasar nan na sake duba dokokin da suka shafi tafi da kamfanonin magunguna a ƙasar nan da nufin ƙarfafa wa ƙananan kamfanoni na gida samar da ingantattun magunguna.
Shi kuwa daraktan kamfanin Pink Blue, Runcie Chidebe, waɗanda suka shirya taron, ya ce tabbas ficewar wasu kamfanonin samar da magunguna daga Najeriya ya ƙara sanya tsadar magunguna, musamman na kansa a ƙasar nan.
Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda da yawa daga cikin masu fama da wannan larura ke gaza siyan magungunan da za su ceci rayukansu tare da yin kira ga gwamnati kan ta duba lamarinsu.