Kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya bayyana sabon farashin litar man fetir a ƙasar.
A wata sanarwa da kamfanin ya aike wa manema labarai, ya ce daga yau Talata 3 ga watan Satumban 2024, kamfanin ya ƙara kuɗin litar man fetir daga naira 617 zuwa 897.
Rahotanni sun tabbatar da cewa tuni wasu gidajen man fetur a Najeriya suka sauya farashin litar zuwa sabon da kamfanin ya sanar.
A jihar Kano dake Arewa maso yammacin Najeriya an ga waɗansu gidajen mai sun mayar da farashin litar man Naira dubu 1 da ɗari 2.
Hakan ta kasance ne kwana ɗaya bayan NNPCL ya bayyana cewa yana fuskantar matsalar ƙarancin kuɗi.
Tuni dai wannan kwarmato na kamfanin NNPCL ya baiwa ‘yan Najeriya satar amsar cewa kamfanin na shirin ƙara kuɗin man ne.