Mai’aikatar ilimi ta jihar Kano ta amince da Ranar 7 ga watan Afrilun da muke ciki a matsayin ranar rufe makarantu na je-ka-ka-dawo da na kwana a faɗin jihar nan.
Don haka, ana sanar da iyaye da wakilansu da ke da yara a makarantun kwana kan su kwasu ‘ya’yansu daga makarantu a gobe da safe.
Sannan a sake buɗe makarantu ne a ranar Lahadi, 30 ga watan Afrilu ga waɗanda ke makarantun kwana, sai kuma Talata, 2 ga watan mayu ga ɗaliban je-ka-ka-dawo, domin fara zangon karatu na uku.
A yayin da yake nuna farin cikinsa game da irin yadda iyaye ke ba da haɗin kai, kwamishinan ilimi na jihar Kano, Ya’u Abdullahi Yan’shana, ya ja hankalin iyaye kan su yi ƙoƙarin dawo da ‘ya’yansu makarantu a ranakun da aka ayyana.
Tare da tabbatar da cewa za a ɗau dukkan matakin da ya dace ga ɗalibai da suka saɓa wa dokar ranar dawowa makaranta.
Sannan ya yi wa ɗaliban fatan za su more hutunsu tare da ƙarasa azumi a agida lafiya.