• Home  
  • Majalisar dokokin Kano ta gabatar da ƙudurin tsige mataimakin gwamnan Kano
- Babban Labari - Labarai

Majalisar dokokin Kano ta gabatar da ƙudurin tsige mataimakin gwamnan Kano

Majalisar dokokin jihar Kano ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam, bisa wasu zarge-zarge da aka gabatar a kansa a gaban majalisar, ranar Alhamis. Shugaban masu rinjaye na majalisar Lawal Hussaini ne ya gabatar da ƙudurin tsige mataimakin gwamnan kan zarge-zarge da suka haɗa da almundahana da kuɗin gwamnati a lokacin da ya […]

Majalisar dokokin jihar Kano ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam, bisa wasu zarge-zarge da aka gabatar a kansa a gaban majalisar, ranar Alhamis.

Shugaban masu rinjaye na majalisar Lawal Hussaini ne ya gabatar da ƙudurin tsige mataimakin gwamnan kan zarge-zarge da suka haɗa da almundahana da kuɗin gwamnati a lokacin da ya shugabanci wasu hukumomin gwamnati.

A kan haka ne majalisar ta ce, kamar yadda doka ta tanada, ta yanke shawarar sanar da mataimakin gwamnan game da matakin da ta fara ɗauka na tsige shi.

A watan Janairu ne gwamnan jihar Kano Abba Kabir ya sanar da sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki a matakin tarayya, daga jam’iyyar NNPP, wadda ya lashe zaɓe ƙarƙashin ta a shekarar 2023.

Sai dai mataimakin nasa Aminu Abdulsalam bai bi shi zuwa jam’iyyar ta APC ba.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai