Majalisar Tattalin arzikin ƙasar nan na gudanar da wani taro a fadar gwamnati da ke Abuja.
Ana sa ran taron zai tattauna batun yadda za a raba tallafin da za a ba wa ‘yan ƙasa domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.
Rahotonni na cewa taron na samun halartar masu rua da tsaki daga bankin Duniya, da sauran hukumomin gwanatin ƙasar.
An sa ran taron zai tattauna batun yadda za a raba tallafin da za a raba wa ‘yan ƙasar, don rage raɗaɗin da cire tallafin man fetur ya haddasa.
An dai samu tashin farashin man fetur a kasar bayan cire tallafin, lamarin da ya kara ta’azzara tashin farashin kayayyaki a ƙasar.
Shugaban ƙasar Bola Tinubu ne ya sanar da bayar da tallafin domin taimaka wa talakawan ƙasar wajen rage musu raɗaɗin da suke fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur ɗin.