Sanatocin kudu maso gabas sun yi kira ga Shugaban Najeriya, Bola Tinubu da ya karrama Farfesa Humphrey Nwosu da girmamawa ta musamman saboda rawar da ya taka wajen shirya zaɓen 1993.
Humphrey Nwosu shi ne shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta a lokacin da aka gudanar da zaɓen 12 ga watan Yulin shekarar 1993, wanda aka soke.
Tun da farko, an yi musayar yawu tare da cacar-baki tsakanin sanatoci a zauren majalisar dattawa, inda mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, wanda ya jagoranci zaman, sannan daga ƙarshe ya sanar da ƙin amincewa da buƙatar.
Daga cikin abubuwan da suke buƙata, akwai sanya wa ofishin INEC na Abuja sunan Humphrey Nwosu, da ba shi karramawa ta ƙasa, da kuma yin shirun minti ɗaya domin girmama shi a majalisar.
Bayan kaɗa ƙuri’ar murya ce, shugaban majalsar ya ce waɗanda ba su amince ba sun fi yawa, don haka ba za a amince da manyan buƙatun biyu ba, amma za a yi shirun minti ɗaya na girmamawa.
Daga bisani ne sanatocin suka nuna rashin jin daɗinsu a zantawarsu da manema labarai, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.
Sun ce ana yi wa Tinubu kallon ‘gwarzon zaɓen 12 ga Yuni’, don haka suke fata ya karrama Farfesa Humphrey Nwosu domin rawar da ya taka a zaɓen.
Jagoran kwamitin sanatocin, Sanata Enyinnaya Abaribe ya ce, “ba don zaɓen ba, da ba za a yi maganar ranar 12 ga Yuni ba.
“Jajircewar Farfesa Humphrey Nwosu ce ta sa aka san wanda ya ci zaɓen, duk da barazana daga sojoji.”