Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa an kashe fitaccen ɗanbindigar nan da ya yi fice wajen garkuwa da jama’a don neman kuɗin fansa, wato Kachalla Isuhu Yellow.
Lamarin ya auku ne da yammacin yau Alhamis, bayan daɗewa da ya yi yana wasan-ɓuya da jami’an tsaro da kuma wasu daga cikin takwarorinsa shugabannin ƙungiyoyin ƴan bindiga a arewacin ƙasar.
Ɗanjarida mai bincike kan harkokin ƴanbindiga, Munir Fura-Girke ne ya tabbatar da kashe ɗanbindigar.
Isuhu ya fi yin fice ne wajen harkokinsa a yankunan Tsafe da Ɗansadau da ke jihar Zamfara.