Wasu Mata magoya bayan Sanata Muhammad Ali Ndume sun yi barazanar yin zanga-zanga tsirara a Majalisar Dokoki ta Kasa, idan ba a mayar da shi kan shugabancin kwamitocin Majalisar Dattawa ba.
Magoya bayan sanatan sun yi wannan barazana ne a lokacin da Ndume ya karbi bakuncinsu tare da sauran magoya bayansa a gidansa da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
A yayin taron ne Sanata Ali Ndume ya bayyana sharadinsa na ci gaba da zama a Jam’iyyarsa ta APC.
A kwanakin baya ne dai uwar Jami’yyar APC na da hannu wajen tsige Ndume daga mukaminsa a Majalisar saboda ya soke Gwamnatin Shugaba Tinubu kan yunwa da tsadar rayuwa da ake fama da su a Najeriya.