Gwamnatin Najeriya ta dauki matakan tsaurara tsaro a iyakokin kasar gabanin zanga-zanga da ake shirin farawa ranar Alhamis ga watan Agusta, 2024.
Shugabar Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa Kemi Nandap, ta ce an tsaurara matakan tsaro a dukkanin iyakokin Najeriya
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Kenneth Udo ne ya bayyana hakan a wata sanarwar da ya fitar a madadin hukumar ranar Asabar.
Kwanturola Janar Kemi Nandap, ta umarci dukkanin shugabannin shiyya-shiyya a Najeriya su yi hattara.
- Mata Za Su Yi Zanga-zanga Tsirara A Majalisar Dokokin Najeriya
- Ƙungiyar Farfaɗo da Arewa Na Goyon Bayan Zanga-zangar Lumana
Nandap ta bukaci hukumar su ƙara sanya ido kan zanga-zangar da wasu ke shirin yi a Najeriya
Shugabar Hukumar ta kuma ce umarnin na da nufin tabbatar da cewa wasu ‘yan ƙasashen waje ba su shigo cikin ƙasar domin shiga zanga-zangar ba.
“Ta wannan hanyar ce za a tabbatar da cewa babu wani baƙon da zai iya fakewa da zanga-zangar don tada zaune tsaye a ƙasar nan,” in ji ta.
Domin tabbatar da cewa ba a samu wata matsala dangaen da wannan aiki ba, hukumar ta dakatar da dukkanin hutun wucin gadin jami’anta domin tabbatar da ba a samu matsala ba a lokacin zanga-zangar.
Kemi Nandap, ta tabbatar wa daukacin ’yan Najeriya shirin hukumar na kiyaye iyakokin ƙasar domin inganta tsaro.